Assalamu Alaikum Yan jarida masu daraja;
- Muna maraba da ku zuwa wannan taron manema labarai a nan Hedikwatar Yan Sanda dake Bompai. Ina kuma gode muku bisa goyon baya da hadin kai da kuke bamu a kowanne lokaci domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Kano.
- Mun shirya wannan taro na manema labarai domin sanar da ku ci gaban da aka samu a fannin tsaro, dabarun da Rundunar ‘Yan Sanda ta dauka wajen yaki da laifuka, da kuma nasarorin da aka samu a kokarin da muke yi na dakile dukkan nau’ukan laifuka a fadin Jihar Kano.
- A zango na uku na wannan shekara ta 2025, mun gudanar da nazari da bincike na musamman akan halin da tsaro ke ciki a wannan Jiha. Bisa ga hakan ne muka kaddamar da wani tsari na musamman mai taken “Operation Kukan Kura” wanda ke nuni da tsayawa tsayin daka bisa tsarin ‘Community Policing’, wato aiki kafada da kafada tare da al’umma, inda jama’a ke bayar da hadin kai ta hanyar samar da bayanai, hana aikata laifi, kiyayewa da kuma magance aikata laifi. Wannan mataki ya yi daidai da umarnin da mai girma Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, PhD, NPM, ya bayar ga dukkan rundunonin ‘yan sanda da su rungumi tsarin aiki kai tsaye tare da al’umma domin magance matsalolin tsaro.
- Manufar wannan sabon shiri shine yin amfani da fasaha da dabaru wajen ganowa da kuma hana faruwar laifuka kamar daba, garkuwa da mutane da fashi da makami a cikin birnin Kano, kan iyakokin jihar Kano, da kuma yaki da sha da fataucin muggan kwayoyi da sauran laifuka. Tun bayan kaddamar da wannan aiki daga ranar 1 ga Yuli, 2025, an samu nasarorin da ba a taba samun irinsu ba.
- Tabbas! Daga jawabinmu da muka baku na ranar 16 ga Yuni, 2025 (kwanaki 24 da suka wuce), mun kama mutane 98 da ake zargi da aikata manyan laifuka guda 21, wanda suka hada da fashi da makami, daba, fataucin miyagun kwayoyi, sata, zamba da dai sauransu.
Abubuwan da aka kwato daga hannunsu sun hada da: Muggan Makamai, Motoci, Adaidaita Sahu da babura da muke zargin na sata ne, Wayoyin hannu, Miyagun kwayoyi, Kudin jabu, da dai sauransu.
Nasarorin da muka samu, sune kamar haka;
WADANDA AKA KAMA:
- Masu garkuwa da mutane – mutum 4
- Masu fashi da makami – mutum 21
- Masu fataucin miyagun kwayoyi – mutum 5
- Ɓarayin motoci – mutum 12
- Masu zamba – mutum 4
- Ɓarayi – mutum 5
- Masu faɗan daba – mutum 47
KAYAYYAKIN DA AKA SAMU NA LAIFI:
- Motoci guda 6
- Adaidaita Sahu guda 8
- Babura guda 10
- Sholisho guda 42
- Sinƙin Tabar wiwi (cannabis sativa) guda 35, sai ƙananan ɗauri guda 1,123
- Madarar Suck and Die Kwalba 86
- Kwayar Exol Sacet 30 da kuma yar ɗiba guda 43
- Kwayar Diazepam Sachet 10 da yar diba guda 53
- Adda guda 16
- Wukake guda 98
- Kudin jabu Dalar Amurka $10,000
- Wayoyin hannu guda 13
- Batirin mota guda 5
- Tayar mota guda 3
- Ko shakka babu, wannan sabon aiki na ‘Operation Kukan Kura’ ana yinsa tare da wasu dabarun aiki na musamman wanda ya hada da tattara bayanan sirri, farmakar wuraren ɓata gari, hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, tattaunawa da shugabannin gargajiya, shugabannin addini, kungiyoyin matasa, Kungiyoyi masu zaman kan su, da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da tsaro mai dorewa.
- A karshe, ina sake jinjina ga jama’ar jihar Kano bisa hadin kai da goyon baya da suke ba rundunar ‘yan sanda. Muna tabbatar muku da cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a Insha Allah. Muna bukatar kowa da kowa ya ci gaba da bayar da rahoto kan duk wani motsi ko abu na laifi zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko ta hanyar kiran wadannan lambobi: 08032419754, 08123821575, 09029292926.
- Ina godiya da kuka bamu lokacin ku. Assalamu Alaikum.
















