Home Security Ɗan Sanda Bashi da damar ɗaukar doka a hannunsa Har Takai ga...

Ɗan Sanda Bashi da damar ɗaukar doka a hannunsa Har Takai ga ya kashe Wanda ake Tuhuma da aikata laifi, inji Barista Hamza

122
0

Hamza N. Dantani Esq

Constitutional Lawyer & Human Rights Activist.27/05/2025

Bana Goyon Bayan Kisan da wasu matasa suka yiwa Marigayi DPO na Rano. Kuma bai kamata Mutane suna Daukan Doka a Hannunsu ba. Wannan Babban Laifi ne.

Amma idan Bera da Sata!

SHIN YAKAMATA YAN SANDA SUN DOKI KO AZABTAR DA WANDA AKE ZARGI DA AIKATA LAIFI HAR YAKAI GA MUTUWA?

Sashi na 214 na Dokar Kasa ( Constitution) da kuma Sashi na 3 na Police Act 2020, shine ya Kirkiri hukumar yan Sanda Nigeria. ( Nigeria Police Force) Sashi na 214 ( 2) (a) ya bawa Yan Sanda tsarin gudanar da aiyyukansu cikin tsari dokoki bisa yadda Dokokin Majalisar tarraya Nigeria ta ayyana! Sashi na 1 na Police Act 2020 ya bayyana cewa Babban Asalin makasudin dokar yan Sanda shine

a- lissafi cikin aminci da Gaskya.

b- Kare Hakkin Dan Adam da kuma Kare Martaban walwalansu.

c- Hadin gwiwa tsakanin su da wasu Jami’an tsaro.

** WASU daga cikin Makasudin Dokar Yan sanda sun hada da:

a. Kare martabar Al’umma and kuma yin Aiki cikin Gaskiya, Adalci da kuma kawo daidaito.

b. Tabbatar da rike mutuncin Hakkin Dan Adam ga ko wane Dan kasa.

c- Da kawo sauyin tunanin mai kyau ga hukumar yan sandan Nigeria ta yadda dan sanda zaiyyi aiki na gari batare da cin hanci ko muzgunawa al’umma ba.

Idan ka duba Sashi na 4 na kundin Dokokin Aikin Dan Sanda, ( Police Act 2020) shine tabbatar da kiyayi Aikata laifi da dukiyar jama’a da kuma kare HAKKIN DAN ADAM wanda yake kunshe a kundin tsarin mulki na Nigeria ( 1999 constitution) da kuma African Charter on Human Rights and People Rights and any other Law;

Idan ka duba shashi na 5 na kundin dokokin yan sanda zaka fahimci yadda ya aka dage wajen anboto akan Kare da mutunta HAKKIN DAN ADAM ga wane dan kasa wanda yake aka tsare shi a wajen yan Sanda ko wata hukumar jami’an tsaro.

A wannan case din a yayi Ajalin DPO na Rano wato Csp Baba Ali wanda ake zarginsa wasu fasatattun matasa da kashe shi wanda Shima DPO ake zarginsa da Azabtar da wani Matashi mai suna Abdullahi har yakai ga kashe shi wanda aka kama shi da zargin ya aikata laifi. ( Suspect)

Bai kamata ace Mutum Kamar DPO ya Azabatar da wani ba har yakai ga kisa, wanda ake zargi da laifi ba, ya sabawa duk wata dokoki na kasa, kuma ya sabawa dokoki na Aikin Dan sanda. Police Act.

Sashi na 34 (1) na Constitution ya bayyana cewa “ ko wane dan kasa yana da Yancin a Martaba shi, kuma yanada yancin mutuntashi, haka zalika babu wanda ya dace a ci zarafinsa wajen dukansa , Azabtar dashi, ko kuma Nakasa shi, ko kuma yi masa wulakanci ko kaskanci.” Haka zalika Sashi na 1 (a) na Kudin dokoki na Yaki da azabtarwa 2017 ( Anti- Torture Act,2017), Ya Gargadi Hukumomi da tabbatar da mutunta da kare Yanci waenda aka Kama ko rikewa a Police Station ko prison. Kuma ya Haramta musu cin Zarafinsu ko Azabtar dasu ta kowane hanya. Kamar Duka, duka da karfi, tsawatarwa, ko kuma tsoratarwa ko kuma saka mishi wata tsaro batare da son ranshi ba.

Marigayi DPO na rano, bai dace a ce yayi duka har da zai hallaka Wanda ake zargi da laifi ba, bai kuma dace ya duke shi ba, wannan ya sabawa dokin kasa da kuma doka na yan sanda. Kuma a hakan manya Kotu sun tabbatar dace ya taba kashe wasu mutane Uku a Bauchi state har aka ci tarar hukumar yan sanda N210,000,000 diyya . Ya taba kashe wasu mutane Guda Biyu a shakarar 2020 Sashi na 36 (4) na Dokar kasar (1999 Constitution) tace , Duk mutumin da aka kamashi, ake zarginsa da aikata laifi, da a kawoshi kotu cikin wasu lokaci Awa 24 idan kuma kotun bata kusa awa 48 ( Kwana Biyu) kamar yadda Sashi na 35 (5) na Dokar Kasa ( 1999 Constitution) yayi bayanin lokiacin.

Yakamata Yan Sanda su rika anfanin da dokokin kasa da kuma na Police Act. Su kiyayi sabawa doka, sun lura da wannan Aikin nasu mai hatsari, don daga karshe shine yake kaisu Aikin da na sani. Ina Mika Ta’aziyya ta Ga iyalen dukkanin waenda suka rasu dakuma Shi Marigayi tsohon DPO na rano da kuma Hukumar yan Sanda . Kuma ina Jan Hankalin matasa da su daina daukan Doka a Hannunsu,

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here