Inyass
Ɗiyar babban shehin Addinin Musulunci Marigayi Khalifa Ishaka Rabi’u wato Jarumar matan ƙasar hausa Haj Ummusalma Isyaka Rabi’u ta raba kuɗadɗen hidimar sallah ga hadiman gidanta.Ummusalma Isyaka tayi wannan rabone a yau a karamar hukumar ta Gwale dake jahar kano don ganin ta samarwa da jama’a makoma tare da raba takardun samun gurbi a makarantar kiyon lafiya don bunƙasa ilimi.
Ummusalma ta yaba da mutane tare da roƙon kan jajurcewa dayiwa shugaban ƙasa dama Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa addu’a da sauke nauyin da Allah ya ɗora musu.Waɗanda suka amfana da wannan tallafin ya haɗarda shuagabancin jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Gwale dana shiya shiya zuwa mazaɓu sai masu mata hidima a kafafen sada zumunta.














