Shugaban Ƙungiyar Comr Shamsu Haruna Aliyu amadadin mambobin Ƙungiyar ta “Tinubu Northern Youths Movement For Continuity 2027” ya taya Malam Nasir Bala Ja’oji murna bisa nadin da aka yi masa a matsayin sabon Sarkin Adon Garin Kasar Hausa, Comr Shamsu ya kira wannan nadi da akayiwa Malam Ja’oji da cewa kyakkyawan karramawar yana nuna sadaukarwar shi ga jagoranci, al’ada, da hidima ga jama’a na Yau da kullum. Muna murna da nadin da aka yi maka, tareda addu’ar Allah ya karawa rayuwa albarka, ya kawo mana zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba a Masarautar Daura da ma wajenta baki daya. In ji Shi
Bikin wanda ya gudana a ranar Lahadi 4 ga watan Mayu na 2025, a masarautar Daura, dake karamar hukumar Daura na jihar Katsina, ya samu halartar manyan baki daga ciki da wajen jihar domin nunawa Malam Nasir Bala Ja’oji kauna, wanda shine Shugaban Ƙungiyar ta Tinubu Northern Youths Movement For Continuity 2027 na kasa baki daya.











