Nidai ma’abocin bibiyar wakokin Hausa ne musamman na dauri duk wayanda suka sanni a zahiri sunsan da haka domin kuwa da wuya naji wata wakar Hausa ta gargajiya ban iya kama sunan mawakin da yayita ba amma a ra’ayi irin nawa ko Dan’Anache da Dan Kwairo sun fi Mamman Shata basirar iya waka da sanin salon zuga mutane a wajena.
Idan aka gangaro kasa-kasa kuwa ni dai a nawa ra’ayin bansan wani mawaki da kasar Hausa ta taba yi wanda yafi Rarara basirar iya waka ba.
Alaji ko baka kaunar Rarara idan anzo fagen waka dole ka sallama masa.











