A Safiyar wannan rana ta Alhamis 20-11-2025.
Zababben Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar karamar Hukumar Birni da kewaye
Engr. Sagir Ibrahim koki yakai ziyara ta musamman ga Babban Daraktan cibiyar kula da Nagartar ayyuka ta kasa NPC
Hon. Dr. Baffa Babba Dan’agundi NIM
Dan yin bangajiya bisa Rakiyar da Daraktan sukayi masa zuwa zauran majalisa tare da godiya ta musamman bisa goyan baya da hadin kai da yake bashi.
Bayan wata tattaunawar da sukayi mai Girma Daraktan yasake bashi Shawarwari musamman na tuntubar dukkanin masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar dake karamar Hukumar Birni dan kara kulla alaka tsakaninsa da Stake Holders din.
Da yake Jawabi Engr. Sagir Ibrahim koki ya nuna farin cikinsa da jin dadinsa bisa wannan Shawarwari da aka bashi kuma yayi Alkawarin yin aiki da Dukkanin shawarwarin da aka bashi tare da daukar aniyar bin Dukkanin masu ruwada tsakin domin ganawa dasu tare da neman goyan bayansu da hadin kansu dan tafiya tare dasu baki daya.

Ayuba Jarimi
SSA MEDIA TO THE DG NPC
Thursday 20,November 2025.










