Kwamitin Gawuna-Garo Strategic Project ƙarƙashin jagorancin Hon. Muhammad Badaru Umar Ungogo
Yau Talata sun bukaci Shugaban hukumar Kula da nagartar ayyuka ta kasa
Hon. Dr. Baffa Babba Dan’agundi Nim
daya jagorance su domin kai ziyara ta musamman da jaddada zumunci ga wanda yayi wa Jam’iyyar APC Takarar mataimakin gwamnan kano a kakar zaben daya gabata
Hon. Murtala Sule Galadima Garo, a ofishin sa dake Babban Birnin Tarayya Abuja.
Da yake jawabi Hon. Dr. Baffa Babba Dan’agundi ya ce sun kawo ziyarar ne domin jaddada zumunci da godiya da dawainiyar da akeyi da mambobin jamiyyar APC dake Kano.
A nasa jawabin Hon. Murtala Sule Galadima Garo ya bayyana matuƙar godiyarsa da murna da wannan babbar ziyara tare da tabbatar da jaddada mubaya’ar sa ɗari bisa ɗari ga wannan tafiya ta Gawuna-Garo, inda cikin maganar sa yake cewa a iya tunanin sa tunda duk nagarta da wata daraja da kuma gogewa kowacce iri ce da ake nema akwai ta a jikin Gawuna kuma akwai ta a jikin Garo, don haka a iya tunanin sa da ganin sa kamata yayi aƙara basu dama, inda ya ƙara da cewa “is a respect for APC ma tace tayi maintaining wannan ticket ɗin.”
A ƙarshe yayi addu’ar fatan Allah ya kauda duk wani mishkila da tarnaƙi da zai iya taɓa wannan tafiya ta Gawuna-Garo mai ɗumbun alkairai,
Allah ya kuma basu gagarumar nasara da sauran duk kujerun Jam’iyyar APC.
yaƙara da fatan Allah ya zaunar da jihar mu ta kano da ƙasar mu Nigeria lafiya da yalwar arziƙi.


Ayuba Jarimi
SSA MEDIA TO DG NPC
Tuesday 7th October 2025.










Masha Allah