A yammacin Wannan rana ta juma’a 03-01
10-2025. Shugaban Ɗariƙar Kadiriyyah na Africa Sheikh karibullah Shiekh Muhd Nasir kabara ya karrama Shugaban Hukumar dake kula da nagartar ayyuka ta kasa Npc.
Muqaddam Dr. Baffa Babba Dan’agundi
Bisa Hidima da dawainiya da yake yiwa Ɗariƙar khadiriyya ba dare ba rana, Shiekh Kariballah yayi wannan jawabi ne lokacin da ake cigaba da tarurrukan Maukibin Qadiriyyah na Africa karo na 75
Dubban Kadirawa ne suka shaida wannan karramawar da Khalifa yayiwa Mukkadam Baffa Babba Dan’agundi.














