Home ENTERTAIMENT RANA BATA KARYA SAI DAI UWAR DIYA TAJI KUNYA Babban Daraktan cibiyar...

RANA BATA KARYA SAI DAI UWAR DIYA TAJI KUNYA Babban Daraktan cibiyar kula da Nagartar Ayyuka ta kasa NPCHon. Dr. Baffa Babba Dan’agundi ya Gwangwaje tsohon shugaban Hukumar NPC Dr. Raji Mustapha da wasu Daraktocin ma’aikatar ta NPC guda biyu da sukayi ritaya daga aiki da Sabbin motoci na zamani

59
1

Idan zaku iya tunawa yau shekera guda daidai dayin handover aiki tsakanin Dr. Raji Mustapha da kuma Dr. Baffa Babba Dan’agundi wanda Dr. Baffa yayi alkawarin zai gayyaci tsohon shugaban dan shirya masa walima ta musamman da kuma alkawarin cigaba da mu’amala dashi cikin mutunci,
yau Shekera guda kenan yau kuma Dr. Baffa ya gayyaci shi tare da shirya masa walima ta musamman da bashi kyautar mota, bayan shi kuma akwai wasu Daraktocin guda biyu sukayi ritaya Dr. Baffa Babba Dan’agundin yayi musu alkawarin cewar duk Daraktan da yayi ritaya daga aiki a ma’aikatar ta NPC zai bashi kyautar mota maimakon ayi musu Gwanjon wacce suke amfani da ita wanda ta gwamnati ce, kuma za’a iya wayar gari babu motocin da za’ayi aiki dasu a ma’aikatar wanda yin hakan ya saɓawa doka hakan tasa Dr. Baffa Babba Dan’agundin yayi alkawarin kyautar mots ga duk Daraktan da yayi ritaya a ma’aikatar kamar yadda kuke gani

  1. Dr. Titilola Oshati da
  2. Resomary Omoyeme
    sunyi ritaya kuma yabasu kyautar mota kamar yadda yayi alkawari kuma yayi musu fatan Alheri.

Taron yasamu Hallartar Dr. Hashim Akko Wanda tsohon Babban Darakta ne na wannan ma’aikatar ta NPC da sauran manyan baki daban, kuma Alhamdulillahi kowa yatafi yana farin ciki tare da fatan Alheri.

Ayuba Jarimi
SSA MEDIA TO DG NPC
Wednesday 10 September 2025.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here