Home ENTERTAIMENT Babban Daraktan Cibiyar kula da Nagartar Ayyuka ta kasa NPC kuma Daraktan...

Babban Daraktan Cibiyar kula da Nagartar Ayyuka ta kasa NPC kuma Daraktan yakin neman zaben Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu mai kula da shiyyar arewa maso yammacin Nigeria Hon. Dr Baffa Babba Dan’agundi

26
0

Babban Daraktan Cibiyar kula da Nagartar Ayyuka ta kasa NPC kuma Daraktan yakin neman zaben Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu mai kula da shiyyar arewa maso yamma
Hon. Dr Baffa Babba Dan’agundi
ya jagoranci wani zama na musamman da Shuwagabannin kungiyoyi da sakatarorinsu na tsawon awanni shida dan jin koke koke da korafe korafe na game da yadda ake jagorantar su a bangarori daban daban da nufin daukar matakin gyare gyare dan kara samar gyara da inganta tafiyar Asiwaju Bola Ahmad Tinubu a jihar Kano

Shugaban ya kuma ware wata ranar danji daga bangaren wanda akayi korafi akansu tare da wanda sukayi korafin, inda nan take aka warware duk wata taƙaddama da kuma samar da daidaito tsakanin bangarorin guda biyu, inda kowa yatafi yana murna da farin ciki da jin dadin yadda zaman ya kasance.

Tabbas wannan abin a yabane kwarai da gaske ace shugaba yana iya zama tare da wanda ake jagoranta dan jin matsalolinsu, wanda a iya sanina babu wani shugaba da yake irin wannan siyasar inba Dr. Baffa Babba Dan’agundi ba

Babban Darakta muna cigaba da yimaka Addu’a ta Musamman akan Allah ya karfafeka yacika maka burinka akan dukkanin wani abu da kasanya a gaba Sabuda kyakkyawar niyyarka ga al’umma da jam’iyyar Apc a Nigeria

31th August 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here