Home ENTERTAIMENT Rukunin kungiyoyi masu goyon bayan jam’iyar APC Cluster 27 karkashin jagoranci Hon....

Rukunin kungiyoyi masu goyon bayan jam’iyar APC Cluster 27 karkashin jagoranci Hon. Abdul Saye Ungogo tsohon dantakarar kansila a mazabar Ungogo dake karamar hukumar Ungogo sun karrama Hon. Dr. Baffa Babba Dan’agundi shugaban hukumar kula da Ingancin Ayyuka ta Kasa( NPC) tare da masu taimaka masa.

37
0

~DG NPC Media.
09-8-2025.

Sun karamma Hon. Dan’agundi a matsayin wanda yake kula da kungiyoyin tun kafun zabe har zuwa yanzu ba tare da ya watsar dasu ba, kamar yadda wasu suke yi, ya cigaba da aiki tare dasu da kuma kawo musu abubuwan cigaba domin yan kungiyoyi su amfana, sun kuma kara ya ba masa akan yadda yake gudanar da almuransa cikin tsari domin ganin jam’iyar APC ta cigaba da samun nasara a zabe mai zuwa na 2027.

Yayin karrama shi, sun kuma karrama Hon. Nasiru Usman Muhammad (Zico) a matsayinsa babban hadimin da yake tsayawa tsayin daka domin ganin duk tsare tsare da ake yi na yan kungiyoyi sun tabbata, wanda suka bayyana Hon. Zico amatsayin kashin bayan samun nasarar yan kungiyoyi. Sun kuma kara karrama Hon. Muhammad Zakariya aminin DG a matsayin jigo wanda shima yake bayar da gudunmawa ko da yaushe dan ganin kungiyoyi masu goyan jam’iyar APC sun yi nasara a kowanne mataki.

Cikin wanda aka karrama harda Sai kuma Hon. Sadiq Babale wanda shine ya jagoranci Cluster din na tsawon shekaru kuma ya tafiyar dasu cikin kyautatawa tare da karamci Sadiq Ado Babale dai tsohon Kansila ne kuma tsohon Adviser a karamar Hukumar Birni,

Yayin gabatar da shaidar karramawa Hon. ZICO ya yabawa Hon. Saye shugaban Cluster 27 a matsayin wanda yake da kokari da kuma rikon amana wajen isar da sako da kuma bin tsari da umarnin da duk aka bayar, yayi kuma kira da dukkan sauran shugabannin rukunin Kungiyar (Cluster) da suyi koyi da Saye wajen yin tsari da kuma yin aiki tukuru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here