Ina miƙa sakon taya murna na musamman ga Shugaban Hukumar Kula da Nagartar Ayyuka ta Kasa (NPC)
Hon Dr. Baffa Babba Danagundi bisa cika shekara ɗaya a wannan matsayi mai muhimmanci.Shekara ɗaya kenan da Allah ya hore maka jagorancin wannan hukuma, wanda cikin ɗan ƙanƙanin lokaci aka fara ganin sauyi da gyara a tsarin gudanarwa, da kuma jajircewa wajen tabbatar da gaskiya da adalci a wannan hukuma.Muna fatan Allah ya ƙara maka basira, lafiya da kwarin gwiwa wajen ci gaba da jagorantar wannan hukuma cikin ƙwarewa da amana. Allah ya sanya wannan shekara daya ta kasance tubalin nasarori da alfanu masu dorewa, ya kuma kara maka nisan kwana cikin cigaba da hidimar kasa. Muna alfahari da kai.
Abdul Saye UngogoS.A Social Media To DG NPCLaraba 16/07/2025
