Home ENTERTAIMENT π’π‡π„πŠπ€π‘π” 52 πŒπ€ 𝐒𝐔 π€π‹ππ€π‘πŠπ€ ...

π’π‡π„πŠπ€π‘π” 52 πŒπ€ 𝐒𝐔 π€π‹ππ€π‘πŠπ€ (𝐇APPY BIRTHDAY 𝐒IR)

102
0

Ayuba Jarimi Mai Taimakawa DG NPC Ɓangaren Kafar Sadarwar zamani

A wannan ranace ta musamman, muna taya ka murnar ranar haihuwar ka, ba kawai domin ka kara shekara a rayuwarka ba, a’a sai domin irin hikimar da Allah SWT ya sanya maka a kirjinka wajen iya jagorancin al’uma a duk inda ka tsinci kanka. Hangen nesanka,gaskiyarka, kyautayinka da kuma kaunar taimakon na kasa da kai sun kasance haske a rayuwar ka kuma sun kasance abun alfahari ne gare mu kasancewar mu masoyanka na hakika.

Yayin da kake bikin cika shekaru 52, ina rokon Allah Madaukakin Sarki Ya ci gaba da ba ka lafiya mai dorewa, farin ciki marar iyaka, da kuma karin nasara a cikin dukkan al’amuran ka a koda yaushe..Allah Ya sanya wannan sabon babi na rayuwa ya zama cike da cikar buri, zaman lafiya, da arziki mai dorewa.Barka da ranar haihuwa, SIR!.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here