A jiya Juma’a ne wani yanki na kasuwar ya kama da wuta wanda yai sanadiyyar konewar kimanin shaguna 250, kamar yadda rahotanni su ka bayyana.
Cikin wani sako da ya fitar a ranar Asabar, Murtala Sule Garo ya yi kira ga gwamnati da manya ‘yna kasuwar jihar da su tallafawa ‘yan kasuwar da gobarar ta shafa.
Garo yai kira da ‘yna kasuwar da su mika lamiransu ga Allah kamar yadda addini ya tanada.
Ya ce, “Ina miƙa sakon jaje da alhini ga ‘yan kasuwa da al’ummar da gobarar kasuwar waya ta Farm Centre a Kano ta shafa.
“Hakika lamarin asarar dukiya babu dadi ko kadan amma babu yadda zamuyi illa mu rungumi jarabawar Allah (SWT) mai dadin ko akasin haka. Kuma na daga cikin cikar imanin mutum karbar kaddara mai kyau ko maras kyau.
“Muna rokon Allah Madaukakin Sarki ya ba su hakuri da juriya, ya mayar mu su da alheri, ya kuma kare afkuwar hakan nan gaba.
“Ina rokon gwamnati da manyan ‘yan kasuwar mu da su taimaka su shiga lamarin wadannan bayin Allah domin a kara farfado da su.


“Allah ya sa hakan ya zamo kaffara kuma ya mayar da alkhairi. Ameen.”










