Home Political BAFFA BABBA DANAGUNDI YA RABA BUHUNA 3000 NA SHINKAFA GA MAMBOBIN KUNGIYOYI...

BAFFA BABBA DANAGUNDI YA RABA BUHUNA 3000 NA SHINKAFA GA MAMBOBIN KUNGIYOYI MASU GOYON BAYAN TINUBU (TSG) A KANO – YA KUMA BAYYANA BABBAN SHIRIN TALLAFI MAI GIRMA ANAN GABA.

59
0

A wani gagarumin yunkuri na tallafa wa al’umma da kuma ƙarfafa magoya baya, Hon. Baffa Babba Dan’agundi, Darakta Janar na National Productivity Centre (NPC), ya raba buhuna 3000 na shinkafa ga membobin kungiyoyi masu goyon bayan Bola Ahmad Tinubu (TSG) a jihar Kano. Wannan rabon ya gudana ne a wani babban taro da ya samu halartar manyan jiga-jigan siyasa daga sassan jihar.

Wannan mataki ya biyo bayan alkawari da aka yi tun lokacin Azumin Ramadan daga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa na Ƙasa, Dist. Sanata Barau I. Jibrin, wanda ya bada gudummawar buhuna 1,000 na shinkafa tare da naira miliyan 20 domin tallafa wa ‘yan kungiya. Duba da yawan wadanda aka tsara zasu amfana da tallafin ya wuce adadin, Sai Hon. Dan’agundi, ya ƙara wasu buhuna 2000, wanda hakan ya kai jimillar buhuna 3000.

A yayin jawabinsa, Hon. Dan’agundi ya jinjina irin matakan farfaɗo da tattalin arziki da shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ke dauka, musamman waɗanda suka shafi rage yunwa da talauci a ƙasar nan. Ya bayyana cewa irin gudummawar DSP Barau wani bangare ne na wannan yunkuri. Haka kuma, ya tabbatar da goyon bayansa da cikakkiyar biyayya ga shugaban ƙasa Tinubu, tare da tabbatar da cewa membobin TSG za su ninka ƙoƙarinsu a zaɓen 2027.

Wannan shirin rabon shinkafa na zuwa ne watanni uku bayan aiwatar da shirin tallafi kashi na farko ga Mambobin tafiyar, a shiyyar Arewa maso Yamma. A cewarsa, wancan da aka yi a baya “somin tabi” ne kawai, domin kuwa akwai babban taron empowerment da ke tafe nan gaba, wanda zai haɗa da raba kayan tallafi kamar haka:

  • Motoci 200
  • Tricycles (Adaidaita Sahu) 100
  • Babura 1,000
  • Firiji masu amfani da hasken rana (Solar Freezers) 1,000
  • Buhuna 1,000 na fulawa
  • Buhuna 1,000 na waken suya (soya beans)
  • Injinan yin taliya 1,000
  • Buhuna 12,000 na shinkafa
  • Keken dinki 500
  • Tallafin ku

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here